Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mutun Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Mutane a wurinda babbar motar daukar mai tayi hadari a Fatakwal. Ranar Alhamis 12 Yuli 2012
Mutane a wurinda babbar motar daukar mai tayi hadari a Fatakwal. Ranar Alhamis 12 Yuli 2012

Wani mutun mai matsakaici shekaru ya tsallake rijiya da baya, bayan da jama’a, suka tara mashi gajiya, bayan da yayi kokarin sace wasu yara, a karamar hukumar Otukpo, ta jihar Benue.

Wanda ake zargin da kokarin sace yaro, suna shi Blessing, an kuma damke shine, a Akpachi, ne dake karamar hukumar Otukpo, ta jihar Benue, alokacin da yake kokarin baiwa yara lemun gwangwani , biskit da madara.

A lokacin da ake tuhumar sa bayan ya sha dukar kawo wuka ya amsa laifinsa na kokarin sace yaran.

Kakakin hukumar ‘yan Sandan jihar ta Benue, Moses Yamu, yace rundunar su bata sami rahoton ba tukun na amma za’a gudanar da bincike .

Blessing, dan asalin jijar Akwa Ibom, yace yayi batar hanya ne akan hanyar san a dawowa daga Fatakwal inda ya halarcin wani horarwa akan aikin malanta.

XS
SM
MD
LG