Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Yankewa Makwabci Kunne


Wani matashi Braide Chinedu, mai shekaru talatin da biyu, ma’aikacin Gwamnatin tarayya, a Fatakwal, ya gurfana a gaban kotu, bisa zargin cewa ya yankewa wani makwabcin mai suna Adelowu Ogundele, kunne.

Wannan dai ya faru ne harabar rukunin gidadjen Gwamnatin taryya, dake Fatakwal, baya wata ‘yar takaddama da ta taso tsakaninsu a bisa wani tushen Ayaba da suke jayayya akai.

Shi dai Chinedu, wanda ake zargin ya farwa Adelowu, da adda ne a lokacin da yake dibar ‘ya’yan Ayabar, dashi Chinedu, yace mallakar sa ne.

Mai shara’a B.M.F Jamabo, ya bada belin Chinedu, akan kude Naira dubu dari hudu, an kuma dage shara’a zuwa mako mai zuwa.

XS
SM
MD
LG