Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Yabawa Shugaba Buhari


Lawal Abdul Faragai

Yau wakiliyar Dandalin VOA ta samu hira da Lawal Abdul Faragai wani dan fafatukar cigaban Najeriya, inda suka tattauna da shi dangane da dawo da ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara, ya ce cigaba ne ya kawo hakan kuma ya kamata al’umma Najeriya su zama masu karbar canjin rayuwa.

Lawal ya kara da cewa mayar da ranar, da shugaba Buhari yayi ya nuna cewar ya cika cikakken dan siyasa da yake harkar siyasar sa ba tare da amfani da kabilanci ba domin tabbatar da hadin kan 'yan Najeriya da cigabansu.

Ya ce Shugaba Buhari ya yi daidai da dawo da ranar 12 ga watan Yuni, kuma yana kira da jan hankalin gwamnati wajen gudanar da bikin ranar baki daya, maimakon yadda aka raya ranar a watan Mayu da kuma yanzu a Yuni.

Ya kara da cewa matasa har yanzu idonsu a rufe yake domin basu san mene ne canji ba, sannan har yanzu basu fuskanci shugabanin 'yan siyasan dake son su ba, kuma akan haka ne yake jan hankalin matasa da su jajirce wajen yiwa shugabanin addu'oi maimakon la’antarsu da ake yi.

Ga cikakken rahoton wakilyar Dandalin VOA Baraka Bashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG