Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa


Wani matashi mai shekaru goma sha tara (19) Andrew Wilson ya harbe mahaifiyarsa Lisa Marie Wilson, mai shekaru hamsin da daya (51) har lahira a dai dai lokacin da take barci.

A lokacin da matashin ke amsa laifin a kotun a jihar Michigan, na Amurka, yace ya harbi mahaifiyar tasa ne biyo bayan wata ‘ya takaddama akan wani kare da matashi ya tsinto ya kuma nemi ya ajiye a gidanta ita kuwa tace bade a gidanta ba sai dai ya kai gidan mahaifinsa.

Matashi wanda da farko ya yiwa ‘yan Sanda masu bincike karyar cewa da ya dawo gida ne ya tarda gawar mahaifiyar tasa ya sheda masu cewa yayi amfani da wata bindiga ce da aka kulle a wurin da aka ajiye wajan hallaka Lisa Marie Willson.

Ana dai tuhumar Andrew da laifin kisa ne da kuma amfani da bindiga ba a bisa ka’ida ba kuma alkali ya ki bada bailinsa zai kuma sake hallara a kotu ranar 28, ga wannan watan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG