Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Dan Najeriya Ya Yi Bajinta A Fannin Kimiyya A Amurka


Hoton kwakwalwa mai lafiya kenan a hagu; kwakwalwa mai cutar Alzheimer kuma a dama.
Hoton kwakwalwa mai lafiya kenan a hagu; kwakwalwa mai cutar Alzheimer kuma a dama.

Matasan Najeriya na cigaba da nuna bajinta a ciki da wajen Najeriya. Yayin da duniya ke yaba natsuwa da da’ar da matasan Najeriya su ka nuna a lokacin zaben Shugaban kasa, wanda har ya kai ga gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da nasara, sai ga shi wani yaro dan asalin Najeriya a nan Amurka, ya yi wani abin tarihi, inda ya gano yadda sinadarin DHA zai iya nakasa cutar kwakwalwa ta Alzheimer.

Bugu da kari, Wannan yaro dan asalin Najeriya mai suna Harold Ekeh mai shekaru 17 da haihuwa, ya na kuma cikin ‘yan zagaye na dab da karshe na wadanda su ka yi nasarar shiga gasar yara masu kwazo na Intel na shekara ta 2015. Kuma saboda bajintarsa a ilimin kimiyya, dukkan fitattun jami’o’in Amurka 8, ciki har da Jami’ar Havard, sun masa tayin dauka.

Rahotanni na nuna cewa Ekeh, wanda ke son zama likitar kwakwalwa zai zabi Jami’ar Yale ce, inda wani yaro dan asalin Ghana mai suna Kwasi Enin, wanda shi ma ya yi irin wannan abin tarihin a baya, lokacin ya na da shekaru 18, ya ke karatu a yanzu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:19 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG