Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Sanda Ya Mutu Yayin Da Rikici Ya Kaure Tsakanin Magoya Bayan Kwallon Kafa


Wani jami'in dan sanda ya mutu a lokacin da rikici ya kaure tsakanin' magoya baya kungiyoyi biyu kafin fara gasar wasan European League tsakanin Athletic Bilbao da Spartak Moscow a filin wasa na San Mames.

Jami'in hukumar 'yan sanda na Basque County, ya bada rahoton cewa dan sandan ya mutu ne bisa bugun zuciya da ya samu yayin da hatsaniyanr ta barke

an tura sama da jami'an tsaro 500 domin tabbatar da tasro, kuma rahotanni sun ce a kalla mutane tara aka kama.bisa faruwar wannan lamari, an kuma tashi a wasan Spartak Moscow ta doke Athletic Bilbao 2-1.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG