Masu bincike a Jami’ar Bern ta k’asar Switzerland sun gano cewa mutane na iya koyon wani harshe a yayin da su ke dogon barci. A baya-bayan nan an wallafa wani binciken a cikin mujallar turanci da ake kira Current Biology da wasu mujallu da su ma duk suka nuna hakan na faruwa.
Maccen da ta jagoranci tawagar masu binciken ita ce Katharina Henke, wata malama a Jami’ar Bern kuma wadda itace ta kirkirocibiyar koyon harsuna da ke jami’ar. Wannan cibiyar ce ta gudanarda gwajin da aka yi a kan matasa maza da mata masu magana da harshen Jamusanci.
Binciken ya gano cewaa lokacin barci, kwakwalwan dan adam na aiki a wnai lokaci, wani lokaci kuma bata yi. Don haka masu binciken sun maida hankali ne a kan lokutan bacci mai nauyi wanda kuma masu binciken su ka ce shine lokaci mai inganci da mutum zai iya koyon abubuwa.
Masu binciken sun yi amfani ne da wani kebantaccen waje don gwaji akan mutanen, yayin da aka rinka s aka musu sautin wasu kalimomi. An rika sanya musu sauti, daya a harshen Jamusanci daya kuma a wani harshen na daban, wanda kirkiro shi aka yi.
Sautukan sun rika maimaituwa ne har sau hudu daya bayan daya. Manufar shine a samar da alaka da zata dade a cikin kwakwalwa a tsakanin harshen Jamusanci da kalimomin jabu da aka kirkiro, domin in mai baccin ya farka ya gane.
A lokacinda mai barcin ya farka, akan gabatar mishi da kalimomin biyu, ta gaskiya da kuma ta jabu – dwadanda zasu, kuma zasu gan su. Ana gwada su ne da sautukan jabu da aka yi amfani da su yayin barcin.
Yayin wannan gwajin, an yi anfani da wata fasahar kimiyya wajen gwada kwakwalen wadanda aka yi binciken a kansu ta hanyar amfani da wata na’ura domin gane aikin kwakwalwansu, a yayin da su ke amsa tambayoyi.
Binciken ya gano cewa yawancin wayanda aka yi binciken a kansu sun bayar da amsan kalmomin daidai fiye da a ce canka kawai su ka yi. Masu binciken sun ce kwakwalwa ta fi gane kalimomi a yayin da bacci ya yi kasa-kasa.
Sai dai kuma masu binciken sun ce ana bukatar karin nazari sosai domin karfafa sakamakon binciken nasu. Abinda dai aka tabattar daga wadannan gwaje-gwajen shine cewa ana iya samarwa da kwakwalwa wani yanayi da za ta iya koyan abubuwa a kowane irin yanayi, a lokacinda mutum yake farke ko yake some.
Facebook Forum