Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakokina Fadakarwa Suke Yi Kan Illar Damfara - Abdulrashid Idris


Fitaccen mawakin Hausan nan a jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya, Abdulrashid Idris, ya ce wakokinsa suna jan hankalin jama'a ne kan irin illolin da ke tattare da damfara.

Yayin wata hira da ya da Dandali, Idris wanda aka fi sani da Hyba Dan Baba, ya ce a yanzu wakokinsa na dubi ne kan wannan matsala ta damfara.

Dalilin haka ya sa ya ce ya kamata ya fadakar da al’umma muhimmancin kulawa tare da yin taka tsantsan saboda gudun fadawa tarkon masu irin wannan aika-aika.

Hyba Dan-baba, wanda wannan shi ne karo na biyu da yake fitowa a zauren Dandali, ya ce kamar mafi aksarin mutane, shi ma ya taba fadawa tarkon ‘yan damfaran duk da cewa ba su yi nasara akansa ba.

Sannan ya kara da cewa wakokinsa na fadakar da matasa kan kira a gare su, da su maida hankali wajen zama masu dogaro da kai.

Wakarsa na isar da sakonnin nasiha da kuma wa’azantarwa na bin rayuwa sannu a hankali,

Mawakin ya kuma jadadda cewar shaye-shaye na tauye kwakwalwa inda ta kan hana mutum zama na gari, yana mai jan hankalin matasan da su kauracewa wannan dabi’a ta shaye-shaye.

Abdulrashid ya kara da cewar a fannin waka dai yana yin wakakokin Hip-Hop da Rap ne.

"Na fara ne sakamakon yadda na taso na ga mawakan hip-hop na yi, kuma kimanin shekaru takwas da suka wuce na fara, amma an fi sani na da wakar da na yi ta “Hyba Dan-baba.”

Daga karshe Hyba Dan-baba, ya ce babban burinsa shi ne, kasuwancinsa ya bunkasa, amma ya ce da kudi ne zai iya bunkasa wakarsa domin a cewar shi, da ruwan ciki akan ja na rijiya.

Sannan ya kara da cewa waka ba ta kawo kudi sosai muddin mutum ba zai hada da wata sana’ar ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:54 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG