Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wainar Da Ake Toyawa A Fannin Wasan Tamola A Duniya


Adrien Rabiot na Paris St-Germain

Kungiyar wasan kwallon kafar Liverpool ta tuntubi mahaifin wakilin dan wasan tsakiya mai shekaru 23, Adrien Rabiot na Paris St-Germain, kan yunkurin ta na dauko shi.

A halin da ake ciki kuma, kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya hana yin amfani da wayoyin salula a filin wasa lokacin da ake gudanar da atisaye.

A Barcelona kuma, dan wasan kungiyar mai shekaru 30, Ivan Rakitic ya ce wasu manyan kungiyoyin wasa sun bukaceshi da ya koma kulob dinsu a wannan lokacin, amma ya yanke shawarar ci gaba da zamansa a Spain.

Kungiyoyi bakwai daga cikin manyan kulob din Turai - ciki har da na Firimiya lig, wadanda suka hada da Manchester City, Chelsea, Manchester United da Liverpool - kididdiga ta nuna cewa sun kashe fiye da fan biliyon 1, wato kimanin yuro miliyan 900 wajan sayen 'yan wasa tun daga shekarar 2010.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG