Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Dan Wasan Kwallon Kwandon Amurka Luol Deng Ya Ziyarci Sudan Ta Kudu


A Lokacin da yake yaro, Luol Deng, da iyayensa da sauran ‘yan uwan sa suka tserewa yakin basasa a wurin da ya zama Sudan ta Kudu a yau. Daga baya ne Deng ya zama tauraro a Kungiyar wasan Kwallon Kwandon Amurka da ake kira NBA a takaice,

A wannan watan na Agusta ne, tsohon dan wasan hukumar kwallon kwandon Amurka da ake kira NBA a takaice, Luol Deng, ya ziyarci kasarsa ta asali, wato Sudan ta Kudu a yanzu. A filin wasan kwallon Manute Bol wanda gidauniyarsa ta gina, ya karfafawa matasa ‘yan wasan kwallon gwiwa ya kuma tattauna da manema labarai game da wasan.

Deng yace wannan wata hanya ce ta kawar da zaman banza da samar da abin yi ga matasa da kuma koya masu muhimmancin yin aiki tare, don haka abin ya wuce wasanni kawai.

A lokacin da yake matashi, Deng da iyayensa da sauran ‘yan uwansa suka tserewa yakin basasar Sudan suka je kasar Masar. A can ne, Deng ya hadu da wani tsohon dan wasan kwallon Kwandon hukumar NBA, tsohon dan rajin samar da taimakon agaji a Sudan ta Kudu kuma, wato Manute Bol, wanda ya koya masa wasan kwallon kwando.

A shekarar 2015, cibiyar Luol Deng ta bude filin wasan Manute Bol a birnin Juba, don tunawa da Bol, wanda ya rasu a shekarar 2010.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG