Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Dan Sanda Ya Lalata Yara Kanana 'Yan Shekaru 5 da 6


An gurfana da wani tsohon dan Sanda mai suna ASP, Yusuf Ibrahim, mai retaya a gaban babban kotun a jahar Bauchi, da laifin yi lalata da wasu yara 'yan shekaru biyar da shekaru shida.

Yusuf Ibrahim, mazaunin unguwar bakin Kura, a Bauchi, ana zargin sa ne da yaudaran yara shiga cikin shagon sa inda ya tafka wannan ta'asar.

Sheda Mai gabatar da kara Mohammad Adamu, ya fadawa kotun cewar wanda ake zargin ya yi anfani da alawar chin gam ne wajan jan ra'ayin yara ne wadan daga bisani ya aikata mugun nufin sa.

Mohammad Adamu, ya kara da cewa laifin ya sabawa sashe na 282, sakin layi {1e} kuma ya tanadi hukunci a sashe na 283, kundin shariar jahar Bauchi.

Yusuf Ibrahim da ake zargin da wannan laifin ya ki bada kai bori ya hau bayan da aka karanta laifin, kuma ana san ran sai shigar da takardan neman bayli.

XS
SM
MD
LG