Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tana Burin Zama Tauraruwa


Amina Ahmad
Amina Ahmad

An bukaci mata dasu hada hannu domin taimakawa juna domin a gudu tare a kuma tsira tare, Amina Ahmad, wata uwa matar aure kuma ‘tar kasuwa ce ta furta haka a hirarsu da wakiliyar Dandalinvoa, Baraka Bashir, a birnin Kano.

Ta ce idan har mata na son ci gaba tilas sai sun hada kai,domin cimma burinsu. Ta kara da cewa a yanzu bukatarta shine ta samu aiki domin taka muhimmiyar rawa a al'ummarta mussamam ma ga rayuwar mata.

Amina Ahmad, ta ce ta karanci harkar kasuwanci a Kano Polytechnic dake jihar Kano, bayan ta nemi gurbin karatu a jam'iar Bayero ta Kano, bata samu ba , da ta kammala karatun nata sai ta fara sana'ar hannu domin dogaro da kai.

Ta ce a yanzu da ta fara neman aikin hakkar ta bata cimma ruwa ba, a cewarta aiki ya zama dan sarki a yanzu, inda take burin zama tauraruwa a cikin alummarta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

XS
SM
MD
LG