Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Swansea City Ta Sallami Bob Bradley


Hukumar gudanarwa na Kungiyar kwallon kafa ta Swansea City, ta fitar da sanarwa Sallamar mai horar da kungiyar mai suna Bob Bradley, bayan kama aikinsa da kwanaki tamanin da biyar a kungiyar.

Hukumar ta bayyana hakan ne jim kadan bayan rashin nasara da kungiyar tayi a wasan firimiya lig da tayi da kungiyar Westham mako na goma Sha takwas, inda Westham, din ta bita har gida ta doke ta da kwallaye 2-0.

Bradley mai shakaru 58, da haihuwa ya kasance dan kasar Amurka na farko da ya taba reke matsayin mai horas da wata kungiyar kwallon kafa bangaren firimiya na kasar Ingila.

Ya karbi ragamar aikine a hannun tsohon kocinta mai suna Francesco Guidolin a farko farkon kakan wasan bana
Swansea City dai a yanzu haka tana mataki na goma Sha tara daga kasan teburin firimiya lig na bana da maki goma Sha biyu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:50 0:00

XS
SM
MD
LG