Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sun Yiwa Masu Shekaru 10 Zuwa 12 Fyade


Hukumar tsaron civil defence ta Najeriya wato (NSCDC) a takaice ta jihar Adamawa ta kama mutane biyar wadanda ake zargin yiwa kanana yara fyade a garin Mubi.

An kama wadanda ake zargin ne sakamakon cune da akayi musu, wadanda ake zargin sun hada da Abdullahi Ibrahim dan shekaru 32, da Musa Muhammed mai shekaru 31, sai Bakura Mohammed mai shekaru 39, Joseph John dan shekara 29 da kuma Mohammed Musa mai shekaru 42.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sanda Sulaiman Baba ne ya tabbatar da kamen da akayi ranar Litinin a Yola, inda yace daya daga cikin wadanda aka Kaman ya amsa laifinsa inda ya sanar musu da cewa wadanda suka fada tarkon nasu yara ne tsakanin shekaru 10 zuwa 12.

Baba ya kara da cewa sakamakon gwajin asibiti ya tabbatar da hakan, kuma yaran mata ne kanana masu talla. Ya ci gaba da yiwa iyaye gargadi akan su guji aika yaran su talla maimakon haka su tura su makaranta.

Za a gurfanar wadanda ake zargin a gaban kotu da lafin fyade, amfani da karfi da tursasa kananan yara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG