Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Suarez Yayi Fice a Yayin Da Man City Tayi Nasara


SOCCER-ENGLAND/(fayal)
SOCCER-ENGLAND/(fayal)

Luis Suarez yayi gagarumar shelar zuwansa fagen kwallon North-West England da jefa Kwallaye biyu cikin farkon rabin awa, to amma kulab din Manchester City bai bar hankoronsa na yin nasara a quarter final ya dusashe ba.

Basalona na barazanar yin fice a rukunin 16 na kofin UEFA bayan da tsohon barden kulab din kwallon Liverpool Suarez ya barrarraka daya bangaren har saun biyu.

A maimakon hakan 'yan City sun yinkuro sannan kuma wani wawan bugun da Sergio Aguero yayi a tsakiyar fili a rabin awa na biyu na nuna cewar har yanzu suna da sauran tasiri.

XS
SM
MD
LG