California kasa ce inda girgizar kasa kan yawan faruwa, kuma yanzu an samar wa mazaunan Birnin Los Angeles wani shirin gargadin jama’a akan sauyin yanayi aduk lokacin da ya dace, musamman bayan bullar alamomin girgizar kasan da akan gani daga raƙuman ruwa na teku in ya doso wa wurinsu.
Wannan sabon tsarin da aka jinkirta fitowarsa, wanda aka kira ShakeAlertLA, shine farkon irinsa a Amurka.
Irin wannan tsarin na gargadin jama’a akan girgizar kasa, zai iya ceton rayukan jama’a masu yawa, in ji Jeff Gorell, Mataimakin magajin garin Birnin Los Angeles dake jagorancin sashen tabattarda zaman lafiyar jama'a, a lokacinda yake nuna yadda manhajar ta ke aiki a wayar salular sa.
"
Lokacin da girgizar ƙasa ta fara bulla, alamar farko da zata fita, ana kiranta P-waves
inji shi. Manhajar zata yi aiki ne a matsayin gargadi ne, maimakon taguwar ruwa mai yin barna ba.”
Tsarin faɗakarwa, wanda ya dogara akan bayanai daga masu auna yanayi a ko'ina cikin yankin, zai iya jan kunne har na tsawon sakanin dakika 90 na gargadi don sanarda al’ummar cewa wata girgizan kasa mai karfin mataki na 5 ko fiye da hakan, tana kan hanya.
Hatta dan lokaci kalilan na da muhimmanci wajen ceton rayukka, a cewar magajin garin birnin na Los Angeles, Eric Garcetti, yayin da yake kaddamarda wannan manhajar ta tafi-da-gidanka ta ShakeAlertLA a watan Janairu. Wannan tsarin ne zai baiwa mutane damar zauna ko su kwanta, su rufe kansu ko kuma su riƙe kansu, kamar yadda aka koya mu susu rinka yi a duk lokacinda ake girgizan kasa.
Facebook Forum