Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Dambace wa Tsakanin Joshua Da Ruiz


Za a yi wata sabuwar karawar damben zamani, tsakanin Andy Ruiz zakaran dambe na duniya da Anthony Joshua a birnin Saudi Arabia.

‘Yan damben biyu za su hadu ne a Saudi Arabia a ranar Asabar, watanni shida bayan da Ruiz ya doke Joshua a wata karawar da suka yi a filin damben Madison Square Garden da ke birnin New York.

Nasarar da Ruiz, ba’amuke dan asalin kasar Mexico, ya samu akan Joshua dan kasar Birtaniya amma dan asalin Najeriya, ta zo wa mutane da dama da mamaki.

Gabanin karawar ta New York, da yawa daga cikin masu sa ido a fannin damben zamani, na yi wa Ruiz kallon dan ajin ‘yan dagaji.

Wannan karawa, za ta zamanto mai cike da sarkakiya, a bangaren guda, idan Joshua ya doke Ruiz, hakan zai sa ya maido da kimarsa a duniyar damben zamani, akasin hakan kuwa, tauraruwarsa za ta kusan daina haskawa baki daya a duniyar ta dambe.

A bangaren Ruiz kuwa, kusan za a iya cewa, ba shi da abin da zai rasa ko da ya sha kaye a hannun Joshua, domin da ma ba karfinsu da ajinsu daya da Joshua ba.

Amma idan har ya samu nasara, tauraruwarsa za ta sake haskakawa fiye da wacce ya samu nasara akan Joshua a karawarsu ta farko a New York.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG