Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shafin Sadarwa na Twitter zai Fara Tattara Bayanan Wayoyin Hannu


Twitter
Twitter

Shafin sadarwa na yanar gizo mai suna Twitter ya bayyana cewa zai fara tattara bayanai kan wayoyin hannu. Shi dai wannan shafin na yanar gizo wato, Twitter mutane na amfani da shi wajen rubuta sharhin ko kuma bayyana abin da ke zukatansu, miliyoyin mutane na amfani da shi.

Idan mutum nada wannan app na Twitter akan waya, to kamfanin nada damar da zai rinka duba duk abin dakasa a cikin wayar ka batare da izini mutane ba, kamfanin yace alokacin daka fara amfani da kayansu ka amince da duk dokokinsu wanda ya hada da karba da tattara bayananka na ciki.

Kamafanin zaiyi amfani da bayanan daya karba domin inganta dangantakar mutane da kamfanin, wajen dubawa da gano me mutane ke bukata don sanin wace irin talla zasu yi maka, misali idan kana da sha’awar wasan motsa jiki to duk yawancin tallar da zasuyi maka zata zamo abubuwan da kake bukatane na motsa jiki.

Amma idan mutane na ganin ana gane musu asiri to akwai fasalin da zai baka damar zaben cewa baka so.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00

XS
SM
MD
LG