Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauran Dakika Talatin Kawai a Kawo karshen karin Lokaci


Amurka da Portugal
Amurka da Portugal
A gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da aka yi jiya Lahadi a kasar Brazil, Portugal ta ci kwallo a karshen wasan ta da Amurka, wanda hakan ya kai su ga yin canjaras biyu da biyu a rukunin su na G.

Portugal ta dirka kwallon ne ana sauran dakika talatin kawai a kawo karshen karin lokacin mintoci biyar da aka yi saboda 'yan tsaye-tskwayen da aka yi cikin wasan da suka yi na mintoci casa'in. Hakan ya baiwa Portugal damar ci gaba da sa rai, a yayin da kuma a yanzu dai, ya hana Amurka kaiwa ga zagaye na biyu.

Da safiyar jiya Lahadi a rukunin H, Belgium ta yiwa Russia ci daya da babu, Aljeriya kuma ta gama da Kuriya ta Kudu ci hudu da biyu.

Idan Aljeriya ta yi nasara a wasan ta da Russia wanda shi ne na karshe a rukunin su, za ta shiga wasan zagaye na gaba. Idan kuma Russia ce ta yi nasara, ta na iya kaiwa ga zagaye na gaba.

Abun ya fi sarkakkiya a rukunin G, wanda ake kira rukunin mutuwa, inda Amurka da Jamus ke jagorantar rukunin da maki hudu, a yayin da Portugal da Ghana ke da maki daya-daya.

Ranar Alhamis mai zuwa Amurka za ta kara da Jamus, Portugal kuma ta fafata da Ghana. Idan Amurka da Jamus suka yi canjaras, dukan su biyu za su kai ga zagaye na gaba.
XS
SM
MD
LG