Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sau Nawa Barcelona Da Real Madrid Suka Kara?


A ranar Lahadi da ta gabata aka fafata a babban wasa na El-classico tsakanin kungiyoyi biyu da ke kasar Spain, Barcelona da abokiyar hammayarta Real Madrid, bangaren gasar La liga na 2018/19 mako na goma.

Wasan ya gudana ne a gidan Barcelona inda ta lallasa Real Madrid da ci 5 da 1.

Wadannan kungiyoyi sun fara karawa a tsakaninsu tun a shekarar 1902, kimanin shekaru 116 kenan da suka wuce.

Ga yadda haduwar wasannin ta su ta kasance a gasar LALIGA a duk ilahirin fafatawarsu sau 176.

Kungiyar Real Madrid ta yi nasara sau 72, ita kuwa Barcelona ta yi nasara sau 70 any i canjaras (draw) sau 34. Real Madrid ta jefawa Barcelona kwallaye guda 285 a ragarta, Barcelona ta jefawa Madrid kwallaye 282 a raga.

A gasar Copa Del Rey kuwa kungiyoyin sun hadu sau 33, Barcelona ta yi nasara sau 14, Madrid ta yi nasara sau 12, an yi kunnen doki (draw) sau 14.

A wasan Copa Del Rey Barcelona ta jefawa Madrid kwallaye 63 sai
Madrid ta jefawa Barcelona kwallaye 64. A gasar Copa De Laliga, na kasar ta Spain kuwa Kungiyoyin sun fafata sau 6.

Barcelona ta samu nasara sau 2, Madrid ba ta taba yin nasara a wannan wasan ba any i draw sau 4. Barcelona ta jefawa Madrid kwallaye 13
Madrid ta jefawa Barcelona kwallaye 8 a raga.

A bangaren Spanish Super Cup sun barje gumi a tsakanisu sau 14, Madrid ta yi nasara sau 8, Barcelona ta yi nasara sau 4, kunnen doki sau 2, Madrid ta jefa kwallaye 30 wa Barcelona, ita kuwa Barcelona ta jefawa Madrid kwallaye 18 a raga.

Sai kuma gasar Zakarun turai UEFA Champions League sun hadu sau 8 inda
Barcelona ta yi nasara sau 2, Madrid ta yi nasara sau 3, kunnen doki sau 3.

Madrid ta jefawa Barcelona kwallaye har guda 13, Barcelona ta jefawa Madrid kwallaye 10, a jimillar wasan gasanni da suka fafata (Competition) sun hadu sau 237.

Real Madrid ce ta yi nasara a wasanni 95, Barcelona ta samu nasara a wasanni 92, sun yi kunnen doki sau 50. Jimillan kwallaye kuwa Real Madrid ta jefawa Barcelona kwallaye 400, a raga. Barcelona ta jefawa Madrid kwallaye 386, a raga.

Sai bangaren wasannin sada zumunci (Freindly) kungiyoyin biyu sun kara sau 34, Barcelona ta yi nasara sau 20, Real Madrid ta yi nasara sau 4 an yi canjaras sau 10.

A jimillar haduwarsu a dukkanin wasanni har da na sada zumunci sun hadu sau 272, Barcelona ta yi nasara a wasanni 113, Madrid ta yi nasara a wasanni 99 an yi canjaras (draw) sau 60.

Yadda jimillan kwallaye ta kama kuwa Barcelona ta jefawa Madrid kwallaye 477, a ragarta sannan ita Real Madrid ta jefawa Barcelona kwallaye 445, a raga.

A wasan na ranar lahadi, an yi shi ne ba tare da zakarun 'yan wasa ba irinsu Cristiano Ronaldo, sakamakon ya bar Real Madrid ya koma Juventus, da kuma Lionel Messi dan wasan Barcelona wadda ya samu rauni a hanunsa, a wasan da kungiyarsa ta Barcelona ta lallasa Savilla da ci 4-2 a wasan mako na tara bangaren La Liga bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG