Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Satar Fasaha Ce Babban Kalubalenmu - Sama'ila Awadeng


Samaila Awadeng

A shirin nishadi yau daga garin Jos a jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya ne, inda wakiliyar DandalinVOA, Baraka Bashir ta samu hira da wani tsohon dan jarida kuma jigo a masana'antar nishadi wanda ya faro aikinsa daga tashar NTA har ya kawo yanzu.

Sama'ila Awadeng dan jihar Filato, darekta ne da ya shafe shekaru kimanin 30 a wannan masana’antar. Ya fara aikinsa ne daga gidan talabijin na kasa wato NTA, kuma tun wannan lokaci ne ya tsunduma ga harkar nishadi.

Ko da yake, ya ce ya fi gwaninta a fina-finan Turanci amma yakan yi fina-finan Hausa domin a cewarsa akwai wani fim mai suna Jamila wanda shi ya ba da umarni, aka kuma saka a tashar satellite ta Movie Magic, baya ga wannan ma, ya ce ya shirya wasu shirye-shirye na raha da nishadi.

Daga cikin kalubalen da ya fuskanta a masana’antar ta nishadi, shi ne matsalar satar fasaha, inda yake cewa kafin ka fitar da shi tuni masu satar fasaha sun sata har sun watsa shi, inda ya ce, wannan babban abin damuwa ne.

Ya kara da cewa hakan ne ke sa masu sana’a fadawa halin wahala da kunci, da kuma rashin samun riba da kwarin gwiwar da zai ba su damar sake wani fim din.

Sama'ila ya kara da cewa a wasu lokutan ma kafin ya fitar da wani shiri da ya yi tuni wani zai sace basirarsa, a canza tsarin shirin a kuma watsa shi ga duniya.

Ya ce duk da wannan matsala bai taba kai karar wani ba, domin ko an kai kara ba’a magance matsalar. Kuma kamun mutumin da ya yi satar fasahar abu ne mai wahalar gaske.

A saurari cikakkiyar hirarsu da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:46 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG