Yawan mutanen da suka biya kudin sabuwar wayar Samsung ta Galaxy S8 sun haura yawan mutanen da suka fara sayen wayar S7 a shekarar da ta gabata.
Duk kuwa da matsalar da wayar kamfanin Samsung ta samu a shekarar da ta gabata inda wayar Galaxy Note 7 ta rika kamawa da wuta, amma hakan bai tsorata masu ‘kaunar wayoyin Samsung ba.
An shirya fitar da wayar Galaxy S8 kasuwa ranar 21 ga wannan wata, a Koriya ta Kudu da Amurka da kuma Canada, ana dai kyautata tsammanin sabuwar wayar za ta taimakawa kamfanin wajen farfadowa daga if’tila’in da ya afka masa a shekarar da ta gabata.
An kayata sabuwar wayar har ma masu saka hannun jari da masu fashin baki ke ganin wayar za ta bayar da mamaki wajen yin cinikin da kamfanin bai taba yi ba ga na’urorin da ya taba fitarwa.
Galaxy S8 zata zamanto wayar da ta fi kowacce rashin hadari a wannan zamani, biyo bayan matakan tsaron da aka dauka domin kaucewa samun matsalar batiri kamar wanda ya samu wayoyin Note 7.
Masu fashin baki na kyautata tsammanin Samsung zai samu ribar da bai taba samu ba cikin watannin Afirilu da Yuni.
A cewar shugaban sashen kasuwanci na Samsung Koh Dong-jin, kamfanin zai yi amfani da wayar S8 wajen farfadowa a China, inda kamfanin Samsung ya yi ‘kasa daga cikin jerin manyan kamfanonin wayoyi biyar, biyo bayan karuwar gasa daga kananan kamfanoni irin su Huawei.