Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samarin Ko 'Yan Matan?


Kamar yadda muka saba gabatar da shirin samartaka a shafin mu na yanar gizo mai adireshi www.dandalinvoa.com, a wannan makon zamu tattauna ne akan yadda samari da 'yan mata kewa juna karya ba tare da jin tsoron yadda zata je ta dawo ba.

Yawancin samari sun bayyana yadda 'yan mata ke dora su a hanyar zama makaryata a sakamakon wasu dalilai da wasu suka alakanta da kwadayin abin duniya da son zuciya.

koda shike wasu daga jikin 'yan matan da muka zanta da su sun bayyana cewar suna gane duk wani saurayi makaryaci, kuma da zarar sun fahimci makaryaci ne, basa bata lokaci wajan yanke hukuncin rabuwa da shi.

Amma babban abin tambaya a nan shine idan samari sun ce 'yan mata ma sukan yaudari samari kokuma yi masu karya, ta yaya hakan ke faruwa?

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG