Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salman Khan Zai Shiga Sahun Masu Haihuwa Ba Aure


Salman Khan
Salman Khan

Da alamar shahararren jarumin fina finan India Salman Khan, zai shiga cikin mutanen da suke haifuwa ba tare da aure ba.

Lallai wannan ba sabon labari ba ne cewar, Salman na kin yin aure tun da dadewa. Sai dai jarumin yace zai haifu amma duk da hakan ya makara. Kowa na sane da yanda jarumin ke sha’awar samun haifuwa kuma yace zai cika shekaru 52 a cikin watan Disamba wannan shekara, don haka shi kansa na ganin lokaci yayi.

Rahotannin sun nuna cewar mahaifiyar Salman Khan tana so ya samu abin haifuwa, yace akwai yiwuwar nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa zai nemi wacce zata haifu masa. Dan wasan yace yana sane da idan ya haifu a yanzu, hakan na nufin a lokacin da dansa zai cika shekaru 20 wato shi kuma ya samu shekaru 70. Salman Khan yace lallai zi yi hakan saboda ya farantawa iyayensa rai.

Tusshar Kapoor shine ya fara wannan salon haifuwa ba tare da aure ba a masana’antar fina finai ta Bollywood a shekarar 2016 yayin da ya haifi dansa Lakshya, bayan haka darekta Karan Johar ya biyo sawu inda shi kuma ya samu yan biyu da suka hada da Yash da Roohi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG