Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin Neman Gurbi A Gasar Kwallon Kafa Na Duniya


A cigaba da wasanin neman gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara 2018, a jiya an fafata a yankin nahiyar turai Inda Kasar Azerbaijan tasha kashi da ci 4-1 a hannun Jamus,

England ta doke Lithuania da kwallo 2-0, San Marino tasha kashi a gidanta da ci 6-0 a hannun Checz Republic.

Armenia ta samu nasara akan Kazakhstan da ci 2-0, Montenegro 1-2 Poland, Romania tayi canjaras 0-0 da Kasar Denmark, Scotland 1-0 Slovenia, Malta nada 1 Slovakia nada 3, Northern Ireland 2-0 Norway.

Haka kuma a yau za'a fafata a wasannin sada zumunci tsakanin kasa da kasa, Inda Kasar Turkey zata gwabza da Moldova Denmark U21 da Kasar England U21 sai Australia U21 da Finland U21, Senegal da Ivory Coast, Italy U21 da Spain U21, Sweden da Republic Checa.

Za'a buga wasannin ne alokota daban daban agogon Najeriya, Nijar, kamaru da kasar Chadi, an kuma dage wasan da Najeriya zata buga da da Kasar Burkina Faso.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

XS
SM
MD
LG