Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakacin 'ya kasuwa da wutar lantarki na cikin dalilan dake haddasa gobara a kasuwanni


Gobara a kasuwa
Gobara a kasuwa

A cikin tattaunawar da aka yi akan yawan barkewar gobara a kasuwannin arewa masu muhawara sun bayyana dalilai da dama da suke haddasa gobara cikinsu har da sakacin 'yan kasuwan da wutar lantarki

Baicin cukoson rumfuna a kasuwanni da 'yan kasuwa ke haddasawa wutar lartanki wadda ake ba jama'a da gurbatattun kaya suna cikin dalilin da ake samun yawan barkewar gobara a kasuwanni.

Kasuwoyi da yawa da suka samu gobara sanadin lantarki ne. Hakan ya faru a kasuwannin Kano da wasu garuruwan arewa. Ita wutar lantarkin cike take da kayan da basu da inganci kamar wayoyin da basu dace ba da makamantansu. Abu ma biye da shi kuma shi ne rashin kulawa daga hukumomin dake bada wuta. Sau tari wani abun lantarkin na bukatar gyara amma sai a barshi sai gobara ta barke a soma guje guje.

Akwai sakacin 'yan kasuwan. Yawancinsu basu damu ba. Haka kuma suna jan wuta ta hanyar da bata dace ba. Suna samun kudi suna cin riba amma basa fitar da zakka da kula da na kasa dasu.

Hukumar kasuwa ita ma tana sakaci. Bata kula da kasuwanni da zara ta raba shaguna. Da yawa mutane na wuce shagunan da aka basu. Kamata ya yi a hukunta duk wanda ya wuce wurin da aka bashi. Haka kuma hukumar bata ajiye 'yan kwanakwana a kasuwa balantana ma ta ajiye jirage masu saukan angulu da zasu kashe gobara da zara ta tashi. Hukumar kasuwa ta ki sabunta kasuwannin kasa yadda zasu zo daidai da zamani.

Ga cikakken bayani.

XS
SM
MD
LG