Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Da Na Sha Fitsarin Wani Dan In Rayu


Wani matashi mai shekaru 28 da haihuwa Nwaka John, da ke cikin tawagar y‘an Najeriya da aka ceto daga kangin bauta a kasar Libya, sun isa jihar Legas da yammacin Alhamis, kuma ya baiyana wa manema labarai irin akubar da ya suka fuskanta a kasar.

Mujallar Daily Post, ta wallafa cewa matashin dake daya daga cikin mutane 157, ‘yan Najeriyar da aka maido gida daga kasar Libya, ya bayyana cewa sai da ya kai ga shan fitsarin wani mutum dan kawai ya rayu.

John, wanda dan asalin jihar Imo, ne yana da digiri a fannin injiniya na na’ura mai kwakwalwa, ya bar Najeriya ne ranar 23, ga watan Yuni, na shekarar 2017, da niyar shiga nahiyar Turai, amma ya tsinci kanshi a wannan kasa dake arewacin Afirka.

Matashin ya ce “na kwashe kwanaki 5 a cikin hamada, daga karshe sai da na sha fitsarin wani mutum domin in rayu”

Ya kuma kara da cewa a cikin mutane 104 da muka kama hanya, 81 ne kadai suka kai kasar Libya, sauran mutane 23, duk su rasu a hanya cikin hamada, daga karshe ya bayyana cewa wannan tafiyar ajali ce kawai.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG