Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Fim Din Baahubali Ya Fito A Bollywood


Baahubali
Baahubali

Fim din Baahubali, kashi na biyu wanda aka jima ana dako sa a Bollywood, ya fito, daga dukkan alamu yana tattare da nasara.

A kwai kuma harshashen cewa wannan fim din zai doke na farko dama wasu fitattun fina finai kamar Dangal, Diwale da kuma Sultan, inda ake ganin cewa zai tabuka abin arziki a “box office”Watau ma’ana a samun kudaden shiga a Bollywood.

Kashin farko na Baahubali, ya fito ne a shakarar 2015, wanda a wancan lokacin ya baiwa mutane mamaki a irin nasarar da fim din ya samu warin karbuwa daga jama’a, ma’abota kallon fina finai a kasar Indiya da wasu sasa na duniya, inda fim din ya kafa tarihi.

Koda yake kashin na farko ya samarda dalar Amurka miliyan goma sha shida ($16M) a fim din wanda akayi da harshen indiyanci.

Ana sa ran cewa wa kashin na biyu na fim din Baahubali,zai samarda makudan kudade fiye da kudaden da ya samar a kashin farko, wanda ya samada da fiye da dala miliyan dari ($100M) daga dukkan alamu ana harsashen cewa wannan zai samarda fiye da dalar Amurka fiye da miliyan dari da ashirin ($120M).

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

XS
SM
MD
LG