WASHINGTON, DC —
A jihar Adamawa Mata sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabe abunda ke nune da cewa a wannan karon mata sun fi maza, kuma wani abun mamaki ma shine cewar al'umomin daga kananan hukumomin Madagali da Michika, wanda ba'a dade da kwato yankin su daga hannun 'yan Boko Haram, ba a wurin zabe suka kwana domin tabatar da ganin cewa sun yi zabe.
Rundunar 'yan sandar jihar Adamawa, tayi amai ta lashe, inda Kwamishinar 'yan Sandar jihar, Mr. Gabriel Adaji, ya bayyana cewa an kafa dokar hana fita daga karfe shida na ranar lahadi, har zuwa ranar talata, amma daga baya sabili da matsin lamba da kin amincewar jamiyyun adawa suka yi a jihar yasa rundunar 'yan Sandan janye wannan doka da ta kafa.