Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Romelu Lukaku Ya Koma Inter Milan


Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta sayi dan wasan Manchester United, Romelu Lukaku akan fan miliyan 72 kimanin dallar Amurka miliyan 87.

Romelu Lukaku ya kammala sauya shekarsa daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zuwa Inter Milan da ke buga gasar Siriya A, a kasar Italiya, akan kudi fan miliyan 72, in ji jarida TalkSPORT.

Dan wasan ya tashi cikin dare zuwa Milan, inda daruruwan magoya bayansa suka yi maraba da shi a filin jirgin sama da misalin karfe 2 na safe, kuma ana sa ran za a sanar da cikakkiyar yarjejeniyar a yau.

A jiya Laraba da yamma, wakilin Lukaku, Federico Pastorello, ya sanya hoton Lukaku a cikin jirgin sama a shafin Instagram tare da taken: "Mun Shirya tashi sama don zuwa Milan", daga filin jirgin saman Brussels.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG