Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Za Ta Biya Makudan Kudi Kan Dan Wasa Eden Hazard


Chelsea ta bukaci cewa kungiyar Real Madrid ta biya ta zunzurutun kudi har Yuro miliyan €100 don mallakar dan wasan Belgium Eden Hazard.

Kungiyar kwallon ta Paris St. Germain tana neman golan Manchester United David De Gea, mai shekara 28, don ya maye gurbin golan Italiya, Gianluigi Buffon, mai shekara 41 da haihuwa.

Dan wasan Liverpool da kuma Netherlands Virgil Van Dijk, mai shekara 27, yana son ya sabunta yarjejeniyarsa. Manchester United ta ce a shirye take ta yi watsi da duk wani tayi da za a yi wa dan wasanta dan kasar Faransa Paul Pogba, mai shekara 26 a duniya.

Hakazalika nan gaba kadan ne United din za ta sanar da sayen dan wasan Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 24, a matsayin dan wasan da za ta saya na farko a kakar bana.

Borussia Dortmund tana fatan dan wasan Jamus Mario Gotze, mai shekara 27, zai sanya hannu a sabuwar yarjejeniya bayan an ruwaito cewa Arsenal tana zawarcinsa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG