Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Sa'a Ne Ya Sa Algeria Ta Doke Mu – Ighalo


Dan wasa gaba na Najeriya, Odion Ighalo, ranar 7 ga watan Oktoba, 2017. / AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI

Yanzu Algeria za ta kara ne da Senegal a wasan karshe a ranar Juma'a yayin da Tunisia da Najeriya za su yi fafatawar neman gurbi na uku a ranar Laraba.

Dan wasan gaba na kungiyar Super Eagles ta Najeriya Odion Ighalo, ya ce rashin sa ‘a ne ya sa ‘yan wasan Algeria suka yi galaba akansu a wasan dab da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Masar.

Algeria ta doke Najeriya da ci 2-1 bayan da suka yi kunnen doki da ci 1-1 a jiya Lahadi.

‘Yan wasan Algeria sun zurawa Najeriya kwallo ta biyu gab da ana shirin kammala wasan.

“Wasan ya yi zafi sosai, kuma mun tafka rashin sa’a a karshen, mun kuma yi rawar gani bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, ina ganin ba mu cancanci wannan sakamakon ba.” Ighalo ya ce a hirar karshen wasa da ya yi da gidan talbijin na CAF wanda aka wallafa a shafinta na Twitter.

Ya kara da cewa, “amma da ma ita kwallo ta gaji haka, sun samu zura mana kwallo a karshen wasa, wannan ya zama abin koyon darasi a gare mu, yanzu sai mu shiryawa neman gurbi na uku.”

Yanzu Algeria za ta kara ne da Senegal a wasan karshe a ranar Juma'a yayin da Tunisia da Najeriya za su yi fafatawar neman gurbi na uku a ranar Laraba.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG