Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahoton Cin Zarafi, Fyade A Motocin Sufuri Na Uber


Tambarin kamfanin sufuri na Uber

Katafaren kamfanin nan na sufuri Uber, ya bayyana cewa ya samu kararraki dubu 3 kan fyade, da kuma cin zarafi, a harkokin sufurin motocinsa a cikin shekarar da ta gabata.

An bayyana wadanan alkaluman ne jiya a cikin wani rahoto mai shafi 84.

Shugaban kula da bangaren shari’a na kamfanin dai, Tony West, ya ce, bayyana wa duniya wannan rahoton da ke magana kan matsalar tsaro ba abu mai sauki ba ne.

Ya ce, yawancin kamfanoni ba sa magana a kan irin abubuwan nan saboda akwai yiwuwar ya zubar da mutuncin kamfanin, "amma mu a ganinmu, lokaci ne da ya kamata mu fara sabon tsari."

Duk da cewar rahoton ya mayar da hankali kan Amurka ne kawai, lamarin ya sa mutane a duk fadin duniya suna saka alamar tambaya kan ko shin babu hadari wajen amfani da motocin uber.

Sai dai kamfanin na Uber ya ce, duk da haka, sama da kashi 99 cikin biliyoyin ayyukan sufurin da suke, sun gudana lami lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG