WASHINGTON, D C —
Sananan mawakin nan Davido, wanda yayi fice wajan nishadantar da matasa da wakokin zaman, yace waka ko kuma duk sana'ar da mutun ke yi ba zai hana neman ilimi ba.
Ya kara da cewa neman ilimi ya zama wajibi masamman ga matasa domin anan gaba kadan su ragamar milki zai kasance a hannun su, saboda haka ya umarci matasa dasu tashi tsaye dan neman ilimi.
Ya furta haka ne bayan da ya kammala karatun sa na digiri wanda a Jami'ar Babcock, wanda yanzu haka yana shirin yiwa kasa hidima.
Jama'a da dama na zaton cewa Davido, zai zagaye kin yiwa kasa hidima, yace sam zai kasance da sauran matasan domin yiwa kasa hidima.