Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP ta Yanka ta Tashi a Jihar Yobe


Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Adamu Maina Waziri dan takarar Gwamna, a jihar Yobe, ya kaddamar da yakin neman zabensa, a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a maimakon a Damaturu, a jihar sa ta Yobe.

Wannan ya biyo bayan zaman sulhun da akai yi ne a Kaduna, da mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, don sassanta ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP a jihar Yobe.

Biyu daga cikin mutane hudu da suka nemi takarar kujerar gwamnan jihar ta Yobe a karkashin inuwar PDP Hassan Kafayos da Ibrahim Talba sunyi watsi da sulhun da aka yi a Kaduna, na dai-daita tsakaninsu da Adamu Maina Waziri, mutum da akace shine dan takarar, sun yi wannan furucin ne a hira da wakilin muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari.

Kaddamar da Kamfe - 2'56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG