Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nishadi Tare Da Salisu Daddy


A yau shirin namu ya sami zantawa ne Malam Salisu Yahaya wanda aka fi sani da Salisu Daddy, mai wakar siyasa da biki da soyayya a da amma yanzu ya koma wakar manzon Allah (SAW).

S. daddy ya ce ya koma wakar yabon ma'aiki ne a sakamakon wani mafarki da ya taba yi na marigayi Umar Abdul'aziz Fadar bege wanda ya sauya masa tunani baki daya. Mawaki ya ce yanayin yadda marigayin ya zo masa a mafarkinne yasa yaji kawai ya cancanta ya koma ya fara rera wannan wakoki.

Daga karshe matashin mai wakar bege ya bayyana yadda mahaifiyar sa ke matukar jin dadin yadda yake rera waka kuma ya kara da cewa shi da kansa yakan ji farin ciki a duk lokacin da yake rera wakokin sa.

Ga cikakkiyar hirar a nan...

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG