Wata sanarwar da hukumar kwallon kafar duniya FIFA ta fitar ranar Alhamis a kan jerin kungiyoyin wasa na kasashen duniya da suka fi kokari na cewar Kungiyar kwallon kafa ta Nigeria Super Eagle ta sauko daga matsayinta na 44 zuwa matsayi na 46.
Ya zuwa watan da ya gabata, Super Eagle da ta taba zama zakarar Afrika sau uku ta ci gaba da rike matsayi na hudu a jerin kasashen Afrika da suka yi fice.
Da ma an yi zaton kungiyar ta Nigeria zata samu koma baya sabili da rashin wasu kwararar harkoki da zai kara mata kaimi a matsayinta na 44 na FIFA a shekarar da ta gabata.
Wasanni biyu da Eagles zata yi a cikin wannan watan Maris, ana sa ran Najeriya zata taka rawar gani, lamarin da zai kaita ga samun matsayin ga a cikin jerin kungiyoyin wasa na kasashen duniya da hukumar FIFA zata fitar a cikin watan Afrilu.
Koda kuwa Najeriya bata samu komai a cikin wadannan wasanni, ba zata rasa kwallaye a cikin wasan shiga gasar cin kofin Afrika na shekarar 2019 da zata yi da kasar Seychelles a garin Asaba, lamarin da zai sa ta samun makin da zasu kaita a jerin kasashen duniya na FIFA.
Kwanaki kalilan bayan wasa da Seychelles, Super Eagles zata fara shirye shiryen yin karan batta da Misra a wasan shiga gasar cin kofin Afrika ta wannan shekarar a nan filin wasan Stephen Keshi dake garin Asaba
Seychelles da Misra dukkanin su suna bayan Najeriya a jerin kasashen da FIFA ta fitar jiya Alhamis da suka fi kokari,inda Seychelles take matsayi na 189, yayin da kuma Misra take matsayi na 57.
A nahiyar Afrika kuwa kasashen Senegal da Tunisia da Morocco da Najeriya da kuma DR Congo sune kan gaba a nahiyar Afrika sa’annan kasar Ghana ta biye ta shida.
Facebook Forum