Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neymar Ya Ce Zata Sauya Zane Game Da Komawarsa Kungiyar Real Madrid


Neymar
Neymar

Tsohon dan wasan Chelsea da Italiya Gianfranco Zola, ya zamo mataimakin sabon kocin kungiyar kwallon Kafa ta Chelsea Sarri.

Zola, wanda ya buga wasa a kungiyar ta Chelsea, a lokacin yana dan wasa ya taimaka wa kungiyar ta lashe kofin kalu bale na kasar Ingila FA Cup Har sau biyu da kuma lig na kasar daga shekara ta 1996 zuwa 2003,

Bayan ajiye takalman wasansa ya zama mai horas da ‘yan wasa inda ya rike kungiyoyin kwallon kafa har uku wadanda suka hada da West Ham, Watford, da kuma Birmingham, kuma ya ajiye aikinsa a watan Afrillun 2017 a kungiyar.

Yanzu haka dai Zola, zai hade da tawagar kungiyar Chelsea, a wasanninta na shirye shiryen lig (Free season) da take yi a can kasar Australia.

Liverpool ta amince da yarjejiniyar sayen mai tsaron raga na Kungiyar Roma mai suna Alisson kan kudi fam miliyan 66.8 Alisson ya kasance mai tsaron raga mafi tsada a duniyar tamola, bayan da ya haura kan mai tsaron ragar.

Gianluigi Buffon wanda aka saye shi yuro 53 a shekara 2001, da kuma Golan Manchester City Ederson, da aka sayeshi yuro miliyan 40 daga Benfica.

Dan wasan Brazil Neymar yace zata sauya zani game da komawarsa kungiiyar Real madrid inda ya bayyana aniyarsa ta cigaba da zamansa a kungiyar PSG in har zasu cigaba da bashi kula ta musamman.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG