Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neymar, Na Kungiyar PSG Na Shawarar Sayen Philipe Coutinho


Neymar da abokan wasan shi na kwallon kafa

Neymar, dan kungiyar kwallon kafa ta PSG ya bayyana sha'awar sa na fatan cewar kungiyarsa ta PSG tayi kokarin ganin ta siyo Phillipe Coutinho.

Dan wasan kwallon kafar kungiyar PSG, Neymar, ya bayyana sha'awar sa ta ganin cewa kungiyar PSG ta sayi dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Barcelona, Phillipe Coutinho, a kakar wasa mai zuwa.

Ana hasashen cewan Neymar wanda PSG ta sayeshi daga Barcelona, zai iya barin kungiyar sai dai idan har kungiyar ta sayi Coutinho, abinda zai iya sa Neymar ya ci gaba da zamansa a kungiyar ta kasar Faransa.

Rahotanni dai sun bayyana cewa tuni dan wasan Neymar, dan kasar Brazil ya fara tattaunawa da shugabannin kungiyar Paris Saint German akan su sayo Coutinho wanda yake shirin barin Barcelona a karshen wannan kakar wasan.

Coutinho ya shafe watanni 18 a kungiyar Barcelona daga tsohon kulob dinsa na Liverpool, sai dai a yanzu Barcelona ta gama yanke shawarar sayar da dan wasan koda kuwa za tayi asarar abinda ta sayeshi daga kungiyar Liverpool sakamakon baya mata abin da ta sa ran zai yi.

Sai dai kungiyar Chelsea, ita ma ta nuna sha'awar sayen dan wasan domin ya maye mata gurbin Edin Hazard, wanda ake tunanin zai koma Real Madrid a kakar wasa mai zuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG