Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Namadi Sambo, ya Kwashe Kwanaki uku Yana Ganawa da ‘Yan Jam’iyyar PDP


Mataimakin Shugaban Najeriya Namadi Sambo
Mataimakin Shugaban Najeriya Namadi Sambo

Yayin da wasu ‘yan jam’iyyar PDP, ke korafi game da zaben fidda gwani da ya gudana a jihohinsu, mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, ya yiwa ‘ya’yan jam’iyyar alwashin tafiya tare.

Mataimakin shugaban kasar ya furta haka ne a wani taron sulhu, da yayi da ‘ya’yan jam’iyyar, PDP, na jihar Yobe, a garin Kaduna. Yace Gwamnati, ba zata bar wani dan jam’iyyar, a baya ba.

Ya kara da cewa “Insha Allahu idan aka yi Gwamnati, za’a yi Gwamnati ne da zata tafi da kowa da kowa babu wanda za’a bari a baya Insha Allahu, na biyu koma muma a matakin tarayya duk wani da yayi takara ba za’a barshi ba shima, harma da wadanda basuyi takarar ba.”

Alhaji Adamu Maina Waziri, dan takarar Gwamna a jihar ta Yobe, da Dr. Adamu Bulama, Ministan dake wakiltan jihar Yobe a majalisar zartarwar tarayyar Najeriya, sun halarci wannan taro na sulhu.

Mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, ya kwashe kwanaki uku ne yana ganawa da ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP ne domin yin sulhu.

PDP sulhu - 4'35"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00

XS
SM
MD
LG