Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Tabbatarwa FIFA Tsayar Da Amaju Pinnick A Matsayin Shugaban NFF


A kokarin ta na kaucewa hukunci dakatar da kasar shiga wasannin kasa da kasa, gwamnatin tarayyar Najeriya, ta bayyanawa hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA sanarwar tsayar da Amaju Pinnick, a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta isar wa hukumar FIFA sakon tabbacin tsayar da Amaju Pinnick, a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, kuma wanda zai ci gaba da tafiyar da al’amuran hukumar tare da aiki da duk masu ruwa da tsaki na hukumar NFF.

Sanarwar ta fito ne awoyi goma sha biyu kafin wa’adin lokacin da hukumar FIFA ta bayar na cewa ko dai Najeriyar ta kawo karshen takaddamar da hukumar kwallon kafa ta kasar ta shiga tsakanin Giwa da Pinnick akan shugabancin hukumar kokuma ta dakatar da ita daga shiga duk wani wasa da ya shafi kasa da kasa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG