Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Fi Mayar Da Hankali Wajan Fina Finan Da Suka Danganci Aure


Ali Rabiu Ali wanda aka fi sani da Daddy, ya ce a masana’antar Kannywood ya fi maida hankali wajen fitar da fina-finai da suka danganci matsalolin da suka shafi lamari na aure.

Jarumin ya kara da cewa abinda ya sa ya fi mayar da hankali ga matsalolin aure yadda al’ummar malam Bahaushe bata baiwa aure muhimmaci ba, hakan ce ta sa fina-finansa suka fi karkata a wannan fanni.

Ya kara da cewa ya taka muhimmiyar rawa a kannywood inda ya ce ya fara tun daga tushe wato rubutun fim da daukar kyammara da rubuta waka da rerata, fitowa a jarumi da kuma bada umarni duk kuwa da cewar a yanzu dai ya fi mayar da hankali a matsayin sa na jarumi.

Daddy ya ce sana’ar fim ta yi masa rana, domin da sana’arce yake rayuwa yake kuma harkokinsa na yau da kullum

kadan daga cikin kalubalen da ya fuskanta a cewar sa, lokacin da ya fara fim ana yi masu mummunar fahimta, hakan har jama’a sukai ta zuga mahaifiyarsa na cewar yaya zata bar danta ya lalace a wannan sana’a da ya shiga.

Hakan ta sa mahaifiyarsa ta kafa masa sharadi bata yarda ta taba hannun mace ba amma dukkanin gurbin da aka bashi ya fito ta amince masa amma banda rike hannun mace.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:18 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG