Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Takwas Sun Rasa Rayukansu A Bikin Maulidi


Rahotani daga jihar Gombe na bayanin cewa mutane takwas sun rasa rayukansu ayayinda wasu mutane goma sha takwas suka samu raunukan a sailin da wata mota da birkinta ya lalace ta takesu a garin Malam Sidi, hedkwatar karamar hukumar Kwami, alokacin da suke jerin gwanon Maulidi.

Kamar yadda kakakin ‘yan Sandan jihar Gombe, DSP Ahmed Usman, ya shedawa wakilin muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad, ita dai motar, ta fito ne daga Gombe zata nufi Bajoga,

Afkuwar haka ke da wuya sai matasa suka kona wannan motar, inda kwamishinan ‘yan Sandan jiharta Gombe, ya bada umarnin kai dauki na gaggawa inda aka aike da ‘yan Sandan kwantar da tarzoma, da kuma kwasan wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti domin samun magani.

Ya kuma bukaci jama’a, da suke bukukuwa na nuna murna dasu kula da bin dokokin hanya domin gujewa afkuwar irin wadannan al’amura da suke faruwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

XS
SM
MD
LG