Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musa Gambo: Mun Bude Makarantar Fina-Finai Mai Bin Tsarin Kasar Amurka


Musa Gambo

A shirinmu na Nishadi, Dandalin VOA ya samu bakunci, Musa Gambo, daya daga cikin jagororin makarantar koyar da sana’o'in harkar fina-finai, wanda ya ce an bude makarantar a shekarar 2016.

Mun bude makarantar koyar da harkar fina-finai bisa tsari irin na kasar Amurka inda ake koyar da dalibai harkar fim a hannu guda, kuma don a samu biyansu kudi kamar yadda ake yi a kasashen waje.

Ya ba da misali cewa bayan an koyar da dalibi zama darakta, makarantar idan ta samu aiki ta hada darakta na ainihi da dalibi ya koyi karatu, za su biya shi kudi na aikin da ya gudanar.

Ya ce makarantar an yi mata rijista karkashin hukumar kula da jami’o'i, sannan suna dauko malamansu ne daga wasu jihohin Najeriya kuma wadanda suka karanci harkar fim ko waka domin samun inganci a harkokin fina-finai.

Ya ce wannan makaranta na samun dalibai maza da mata, kuma daga cikin ka’idojin da ake bukata sai dalibi ya tabbata yana da cancanta ta makin "credit" guda biyar, kafin a ba shi gurbi a makarantar.

Sannan da zarar an kammala diploma ko certificate, dalibi na da damar samun gurbi a jami’a kai tsaye.

Kamar kowacce makaranta, ya ce sukan fuskanci matsalar sai dalibi ya bi dukkanin ka'idoji sai kwatsam, dalibin ya daina zuwa. Sai suka gano cewa iyayensu ne suke hana su, ko sun sami gurbi a wata jami’a.

A saurari cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:10 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG