Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin Daren "Lailatul Kadr"


Ibada cikin dare

Hira da Malam Abba Ibrahim Abubakar a kan muhimmancin daren Lailatul Kadr ga Musulmi.

Yau DandalinVOA ya tattauna da Malam Abba Ibrahim Abubakar, dangane da "Daren Lailatul Kadr," dare mai muhimmanci wanda kowane musulmi ya tabbatar da shi, kuma dare ne da ake samu a watan Ramadana sannan samun sa a dararen mara.

Ya kaar da cewa, manzon Allah ya ce ana bukatar musulmi ya raya dukkanin daren goman karshe watan Ramadana domin dacewa da riskar daren tun da ba’a bayyana wane dare ne takamaimai na lailatul kadr ba.

A cewar Malam Abubakar, dare ne da duk abin da mumini ya roki Allah yake tabbatar masa da shi.

Sannan ya kore jita-jitar da wasu ke yadawa cewa, ana ganin dakin Ka’aba ko bishiyoyi suna sujjada a daren.

Saurari cikakken hirar da Baraka Bashir ta yi da Malamin:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:06:46 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG