Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mourinho Ya Bukaci Manchester United Ta Sayo 'Yan Wasa 5


Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana rashin jin dadin sa musamman ganin yadda aka bar kungiyar a baya wajan musaya da cefano sababbin zaratan 'yan wasa a kakar bana.

Da yake jawabi bayan kungiyar Liverpool ta lallasa kungiyar sa da kwallaye 4 - 1, a wasannin cin kofin kasa daasa na International Championship (ICC) jiya Asabar, Mourinho ya bayyana cewar ya ba kungiyar sa sunayen wasu 'yan wasa guda biyar da yake bukatar kungiyar ta saya.

Amma Kawo yanzu, Fred Diogo Dalot, da Lee Grant, ne kadai suka isa kungiyar, kuma gashi za a kulle kasuwar musaya da cinikayyar zaratan 'yan wasan kwallo ta wannan kakar ranar 9 ga watan Agustan wannan shekarar.

Mourinho, ya kara da cewa "na yi matukar so ace na sake samun karin asu 'yan wasa akalla ko da guda biyu ne".

Ya ce, na bada sunayen'yan wasa biyar da nake bukata a kungiyar tun watannin da suka gabata amma na ji shiru, tana iya yiwuwa in sake samun karin guda, idan haka ta yiwu to, idan kuma bata yiwu ba to ba matsala zamu ci gaba da aiki da 'yan wasan da muke da su kasa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG