Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mikel Arteta Na Gab Da Maye Gurbin Wenger


Tsohon dan wasan tsakiya na Arsenal, Mikel Arteta, na dab da kasancewa Sabon Kocin kungiyar sakamakon cigaba da ake samu wajan daidaitawa da bangarorin kuma indan hakan ya kasance, dan wasan zai maye gurbin Arsene Wenger, wanda ya ajiye aikinsa a karshen kakar wasan bana bayan ya share shekaru ashirin da biyu a kungiyar.

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya yi watsi da batun kiran da kungiyar Chelsea, ta ke masa na yazo ya maye mata gurbin kocinta Antonio Conte.

Mauricio Pochettino, ya ce yana murna da zamansa a kungiyarsa ta Tottenham, a yanzu haka.

Arsenal ta fara tattaunawa da dan wasan Nice Jean-Michael Seri, kan dawowarsa kulob din wadda darajarsa ta kai fam miliyan 40. Itama Chelsea, tana bukatar ganin ta dauko dan wasan.

Manchester united, ta ce tana da karfin guiwa wajan ganin ta dauko dan wasan baya na Tottenham, Toby Alderweireld, inda zata kashe fam miliyan 40 kan sayen dan wasan.

Dan wasan kasar Spain da Barcelona Andres Iniesta, mai shekaru 34, da haihuwa ya ce batun komawarsa kungiyar Manchester City, ba abune mai yuwaba.

Duk da kasancewar tsohon kocinsa a Barcelona Pep Guardiola, wanda yanzu ya ke Kocin Manchester city, ya nuna sha'awarsa kan dan wasan wanda aka alakantashi da komawa lig na kasar Sin a karshen kakan wasan bana.

Real Madrid ta ce ta shirya domin dauko mai tsaron raga na kungiyar Chelsea Thibaut Courtois, dan shekaru 26 a duniya duk da yana da sauran watanni 12 a yarjejeniyar kwantirakinsa da kungiyar Chelsea.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG