Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Kuke Gani Akan Wannan Mataki Da Shah Rukh Khan Ya Dauka Akan Diyarsa?


TAMBAYA: Shararren Jarumin nan na Bollywood, Shah Rukh Khan, ya gindaya sharudda ga duk wani saurayi da yake son ‘yarsa Suhana, Shah Rukh Khan, dai ya dade yana sa ido aka samari dake zance da ‘yar tasa.

Jarumin yace tun tashinsa kawo yanzu da kuma matan da yayi hakokin fina finai dasu ya koyi darussa da dama, hakikanin gaskiya, sharuddan da Shah Rukh Khan, ya gindaya akan ‘yarsa suna da tsauri. Me kuke gani akan wannan mataki da Shah Rukh Khan ya dauka akan diyarsa?

Ana iya aiko mana da sakon amsar wannan tambaya, ko kuma duk ra'ayoyinku kan abinda suka shafi matasa ta email zuwa ga Dandalinvoa@voanews.com

Ana iya ziyartar shafinmu na WhatsApp mai lambar waya +12025775834, "Dandalin VOA Hausa Group" ta yadda zaku rika aiko mana da sakonnin muryoyinku cikin sauki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG