Kowane mai rai na bukatar Soyayyar gaskiya, sai dai mutane kadan ne ke sa’ar gamuwa da masoyan gaskiya a cikin dan kankanin lokaci.
Ya zaka bayyana saoyayyar gaskiya?..
Soyayar gaskiya aba ce da tafi komi dadi da kuma faranta ma dan adam rai a lokacin da mutum ke cikin soyayya.
Dan kawai ka hadu da wani ko wata waddan kake kauna ba shine soyayayyar gaskiya ba, ko da wanda kake so ma najin irin yadda kake ji ba lallai son gaskiya ne ba.
Amma bincike ya nuna hakan shine mataki na farkon soyayyar gaskiya.
A cikin mataki na farko akwai yadda, domin kuwa babu soyayyar da zata kai labari idan babu yadda a tsakanin masoyan.
Idan yadda ta shiga tsakanin masoya, to lallai babu sauran wata damuwa ko tunani na daban akan abokin soyayya.
Amma idan yaddar bata zo daidai ba, to ana iya samun matsala ko kuma rabuwa.
Soyayyar gaskiya abuta ce tsakanin saurayi da budurwa ko mace da namiji mai karfin gaske, saboda idan kana matukar so da kaunar masoyin ka dole ne ka zama abokin sa ko ita.
Masoyin ka dole ya kasance wanda zai iya neman shawara daga gare ka kuma dole ya zamo wanda zai iya aje sirrin ka.
Mu hadu a shafin mu na facebook.com/dandalinvoa domin jin ra'ayoyin ku.