Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawaka Nada Matukar Tasiri Ga Rayuwar Al'ummarsu


Umar Faruk

A yau mun sami bakunci mawakin hip hop na Hausa wato Umar Faruk, wanda aka fi sani da Speysh Graphic, baya ga waka yana harkokin da suka danganci zane-zane akan na’urar mai kwakwalwa da sauransu wato Graphics.

Ya ce, ya tsunduma ga waka ne sakamakon shi mutum ne mai son fadakarwa, kamar yadda gwarzonsa ‘Dabo the Prof’ the su ‘Nexus’ ke yi wa alummarsu; wanda hakan na daya daga cikin ire-iren wakokinsa, yana kuma isar da sakon da yake so.

Kamar misali akwai wata wakarsa wacce ya wake irin mutanen da suke son abin duniya, ko wasu mata da su dai burinsu ka samu su ci, amma su nasu su kadai ne zasu ci ba tare da sun baiwa abokansu ba.

Ya ce mawaki wani mutum ne da zancensa ke da matuka tasiri ga al'ummarsu, don haka ne yake cewa mawaki ba abun rainawa bane.

A bangaren mawakan kuma suma da tasu matsala inda wasu mawakan kan raina mawakan, da suka raine su ta hanyar rashin basu girma da zarar ya tsinci kansa yana da dimbin masoya.

Babban burinsa dai a harka ta waka ya ce shine ya taka wata matsaya, ya kuma samu wata damar da zai taba rayukan mutane ta hanyar da ta dace.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG